Sudan

AU ta bukaci majalisar sojin Sudan da masu zanga zanga su koma teburin tattaunawa

Masu zanga-zanga a kasar Sudan
Masu zanga-zanga a kasar Sudan REUTERS/Umit Bektas

Masu shiga tsakani daga kungiyar kasashen Afrika ta AU sun bukaci majalisar sojin Sudan da shugabannin masu zanga zanga da su koma teburin sasantawa yau laraba, domin kafa gwamnatin da zata jagoranci kasar.

Talla

Jakadan kungiyar kasashen Afrika, Mohammed El Hacen Lebatt yace sun gayyaci bangarorin biyu domin ganawa yau laraba, kuma sun shirya inda za’a gudanar da taron.

Tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ta rushe ne a watan Mayu kan wanda ya dace ya jagoranci gwamnatin rikon kwaryar da kuma adadin wakilan da kowanne bangare ya dace ya samar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.