Isa ga babban shafi
Libya

MDD tayi tur da kisan bakin-haure 44 a Libya

Sansanin tsare bakin-haure da aka kaiwa farmaki ta sama da jiragen yaki a birnin Tripoli.
Sansanin tsare bakin-haure da aka kaiwa farmaki ta sama da jiragen yaki a birnin Tripoli. AFP / Mahmud TURKIA
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Majalisar dinkin duniya hadi da kasashe da dama, sun yi Alla Wadai da kisan gillar da aka yiwa bakin-haure sama da 40, a wani sansani da suke tsare a Libya, bayan harin da aka kai musu ta sama.

Talla

Tuni dai gwamnatin Libya da majalisar dinkin duniya ke marawa baya ta dora alhakin harin akan Janar Khalifa Haftar da ke son kawar da ita.

Jakadan majalisar dinkin duniya a kasar ta Libya, Ghassan Salami, ya bayyana harin a matsayin lafin yaki, tare da bukatar gudanar da binciken kasa da kasa don gano wanda ya bada marnin kai harin, wadanda suka kaishi, da kuma wadanda suka samar da makaman da aka yi amfani da su.

Ita ma dai Turkiya da ke goyon bayan gwamnatin ta Tripoli da kasashen duniya ke marawa baya, bukatar gaggauta gudanar da bincike kan farmakin.

Akalla bakin-haure 44 ne suka halaka a farmakin jiragen yakin na daren jiya Talata, yayinda wasu 130 suka jikkata a sansanin da suke tsare a birnin Tripoli.

Koda yake har yanzu babu wanda yayi ikirarin kai harin, gwamnatin Libya da ke Tripoli ta dora alhakin kan Khalifa Haftar babban kwamandan rundunar soji mafi-karfin-fada-a-ji a kasar, wanda a watan Afrilu ya kaddamar da farmakin hambarar da gwamnatin ta Tripoli da majalisar dinkin duniya ke marawa baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.