Libya

Wani harin sama ya hallaka yan gudun hijira a Tripoli

Ana ci gaba da gwabza fada a Libya
Ana ci gaba da gwabza fada a Libya REUTERS/Ismail Zitouny

Akalla mutane 40 suka mutu sakamakon wani kazamin harin sama da ake zargin dakarun Khalifa Haftar da kaiwa sansanin yan gudun hijira dake Libya.

Talla

Wannan kazamin harin na zuwa ne a daidai lokacin da Janar Khalifa Haftar ke dada jaddada aniyar sa ta karbe iko na birnin Tripoli, bayan kaddamar da munanan hare hare sama da watanni uku da suka gabata.

Mai Magana da yawun hukumar agajin gaggawa Osama Ali yace bayan mutane 40 da suka mutu a cikin wannan harin, wasu 70 sun jikkata, yayin da ake cigaba da zakulo gawarwaki.

Jami’in yace akalla baki yan gudun hijira 120 ke cikin sansanin lokacin da aka kai harin.

Shugaban gwamnatin Libya da kasashen duniya suka amince da ita Sarraj Fayez ya zargi Janar Haftar da kai harin da ya bayyana shi a matsayin laifuffukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.