Sudan

Majalisar sojin Sudan da masu zanga-zanga sun cimma yarjejeniya

Zaman sulhunta rikicin kasar Sudan a Khartoum
Zaman sulhunta rikicin kasar Sudan a Khartoum AFP

Shugabannin majalisar sojin Sudan tare da shugabannin masu zanga zanga sun amince da shirin kafa gwamnatin rikon kwarya wanda za’a dinga kama kama tsakanin bangarorin biyu na shekaru 3.

Talla

Wannan yarjejeniyar na zuwa ne kwana biyu bayan fara wani taro da kungiyar kasashen Afirka da kuma gwamnatin Habasha dake shiga tsakani suka shirya.

Mohammed El Hacen Lebatt na kungiyar kasashen Afrika na AU ya ce bangarorin biyu sun amince su kafa gwamnatin rikon kwarya da zasu dinga karba karba wajen shugabancin ta tsakanin sojin da fararen hula.

Ita dai wannan sabuwar gwamnati da za’a kafa zata kwashe shekaru 3 a karagar mulki kafin gudanar da zabe, yayin da soji zasu jagorance ta na watanni 18, kafin mikawa fararen hula suma su rike na watanni 18.

Mataimakin shugaban majalisar sojin, Janar Mohammed Hamdan Dagalo ya bayyana cewar suna tabbatar wa ‘yan siyasar kasar da kuma kungiyoyin dake dauke da makamai da suka sanya hannu wajen juyin juya halin kasar, cewar wannan yarjejeniya ta shafi kowanne bangare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.