Afrika

Yan Najeriya sun mutu a wani harin sama a Libya

Dakaru dake fada da junan su a Libya
Dakaru dake fada da junan su a Libya REUTERS/Hani Amara

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar yan kasar guda 9 na daga cikin baki 44 da aka kashe a Libya lokacin wani harin sama da ake zargin dakarun Janar Khalifa Haftar da kai wa.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar da cewar, binciken da jami’an diflomasiyar kasar suka kai wurin da aka kai harin ya tabbatar da haka.

Ko yaya za’a iya magance irin wannan tafiya mai hadari, wannan itace tambayar da muka yiwa Malam Muhammad Hashim Suleiman.

Harin sama na Libya ya rutsa da yan Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.