Libya

Mutane dubu 1 sun halaka a sabon yakin Libya

Wasu yan gudun hijira daga kasashen Afirka, zaune a harabar sansanin Tajoura dake Tripoli, da jiragen yaki suka kaiwa farmaki. 2/7/2019.
Wasu yan gudun hijira daga kasashen Afirka, zaune a harabar sansanin Tajoura dake Tripoli, da jiragen yaki suka kaiwa farmaki. 2/7/2019. Reuters

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, ya bukaci tsagaita wutar yakin da ake fafatwa a Libya, tsakanin sojin gwamnatin Fayez Al-Sarraj da kasashen duniya ke marawa baya, da dakarun Janar Khalifa Haftar mai rike da yankin gabashin kasar.

Talla

Kiran na majalisar dinkin duniya ya zo ne bayan da adadin mutane dubu daya suka halaka, a dalilin sabon yakin da aka shafe watanni uku ana gwabzawa, a kokarin da Haftar ke yin a kwace iko da birnin Tripoli, hedikwatar gwamnatin ta Libya.

Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, ya nuna cewa, akalla mutane dubu 5 yakin ya jikkata, wasu sama da dubu 100 kuma suka tsere daga muhallansu, bayaga bayaga hasarar rayuka dubu guda.

A ranar talata, 2 ga watan Yuli, wani farmakin jiragen yaki kan sansanin Tajoura dake birnin Tripoli, ya halaka 'yan gudun hijira 53, wanda tuni gwamnatin Al-Sarraj ta dora alhakin kan dakarun Janar Haftar, zargin da ya musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI