Sudan

Gwamnatin Soji ta sha alwashin tabbatar da sabuwar yarjejeniyarsu

Daruruwan jama'ar Sudan da ke murna bayan cimma yarjejeniya tsakanin bangaren soji da fararen hula
Daruruwan jama'ar Sudan da ke murna bayan cimma yarjejeniya tsakanin bangaren soji da fararen hula REUTERS/Umit Bektas

Gwammnatin mulkin Soji a Sudan ta sha alwashin tabbatar da sharuddan da aka cimma karkashin yarjejeniyar tafiyar da mulkin hadakar kasar tsakaninsu da fararen hula.

Talla

Janar Abdel Fattah al-Burhan da ke jagorantar gwamnatin, ya ce za su tabbatar da cewa daga bangarensu ba su yiwa yarjejeniyar kafar angulu ba, don ganin an samu dorewar zaman lafiya a kasar.

A karkashin yarjejeniyar, bangaren sojoji ne zai jagoranci gwamnatin hadin gwiwar na tsawon watanni 21, daga bisani kuma bangaren farar hula ya karashe shugabancin ragowar watanni 18.

Da safiyar jiya Juma’a ne dai bayan shafe kwanaki biyu bangarorin biyu na tattaunawa, da taimakon kasar Habasha da wakilan kungiyar kasashen Afrika AU, aka cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa da zata shafe shekaru 3 da watanni 3 kafin mikawa farar hula mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI