Wasanni

Gasar Afrika: Mai rike da kofi da mai masaukin baki sun sha kaye

Tauraron kwallon kafar Masar Mohamed Salah, yayin jimamin nasarar da Afrika ta Kudu ta samu a kansu.
Tauraron kwallon kafar Masar Mohamed Salah, yayin jimamin nasarar da Afrika ta Kudu ta samu a kansu. Getty Images

Afirka ta Kudu ta tsallaka zagayen kwata final na gasar kwallon kafa ta nahiyar Afrika bayan fitar da Masar, mai masaukin baki daga gasar da 1-0.

Talla

Dan wasan Afrika ta Kudu Thembinkosi Lorch ne ya jefa kwallon daya tilo cikin ragar Masar yayinda ya rage mintuna 5 a tashi daga wasa.

A jiya asabar din ne kuma Najeriya ta hannun ‘yan wasanta Ighalo da Alex Iwobi, ta doke Kamaru mai rike da kofin gasar, da 3-2.

Kididdiga ta nuna cewa sau 19 aka fafata tsakanin Najeriya da Kamaru, inda Najeriya ta samu nasara a wasanni 11, Kamaru kuma ta lashe 3 daga ciki, yayinda kuma suka yi canjaras ko kunnen doki sau 5.

A halin yanzu Najeriya za ta fafata da Afrika ta Kudu a zagayen kwata final na gasar cin kofin nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI