Wasanni

Shugaban hukumar kwallon kafar Masar yayi murabus

Shugaban hukumar kwallon kafar Masar da yayi murabus, Hani Abou Rida.
Shugaban hukumar kwallon kafar Masar da yayi murabus, Hani Abou Rida. Egypt Today

Shugaban hukumar kwallon kafar Masar, Hani Abou Rida ya ajiye aikinsa jim kadan bayan da kasar ta fice daga gasar cin kofin kasashen Afirka a ranar asabar.

Talla

Kafin ajiye aikin nasa dai, sai da Abou Rida ya kori mataimakansa, biyo bayan kayen da yan wasan na Masar suka sha a hannun Afrika ta Kudu da 1-0.

Daga shekarar 2016 Rida ya soma jagorantar hukumar kwallon Masar, kuma a karkashinsa ne kasarta ta fice daga gasar cin kofin duniya a zagayen farko na matakin rukuni.

Nasarar ta Afrika ta Kudu kan Masar ta kawo karshen sanya mai masaukin bakin da ake cikin kasashen da ake saran za su iya lashe gasar ta bana, wadda a baya Masar din ta lashe kofinta harsau bakwai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.