DR-Congo

Laifukan yaki sun tabbata kan tsohon madugun 'yan tawayen Congo - ICC

Tsohon madugun 'yan tawayen congo Bosco Ntaganda
Tsohon madugun 'yan tawayen congo Bosco Ntaganda Bas Czerwinski / ANP / AFP

Kotun hukumta manyan laifuka ta duniya ICC ta samu tsohon shugaban mayakan kasar jamhuriyar demokradiyar Kongo Bosco Ntaganda, da aikata laifukan kisan gilla ga fararen hula, yi wa mata fyade tare da saka kananan yara aikin soja.

Talla

Mai lakabin suna Terminator", Bosco Ntaganda, mai shekaru 45, ya taka muhimmiyar rawa wajen aikata laifukan cin zarafin fararen hula da aka aikata a shekarar ta 2002-2003 a yankin Ituri dake arewa maso gabashin kasar yankin da ke dankare da arzikin karkashin kasa, kuma yake fama da tashe - tashen hankulla a cewar kotun.

Fyade da kuma bautar da mata ta hanyar jimaí, saka yara yan kasa da shekaru 15 ayukan soja, kisan limaman addinin krista: yanayin kidima ne ya bayyana kan fuskar mutanen da da aka gabatar a gaban zaman kotun na yau, a ci gaba da gudanar da dogon jerin shari’ún tashe tashen hankulan da aka aikata a kasar ta Congo

Kai tsaye Ntaganda ya bada umarnin kashe fararen hula masu yawa, ya gudanar da cikakken aikin soja haka kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa wani kakkarfan gungun mayaka tare ma da korar alúmma daga garuruwansu, a cewar alkali Robert Fremr.

Alkalan kotun ta CPI da ke da cibiya a birnin La Haye na kasar Hollande ta samu dan kongon da aikata laifukan yaki 18 da kuma aikata kisan alúmma, fyade da dangoginsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.