Wasanni

Zafin naman Bafana Bafana zai jigata Super Eagles - Mohlala

Dan wasan Afrika ta Kudu Thembinkosi Lorch, yayin kokarin zarta takwaransa na Masar Walid Soliman a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 2019.
Dan wasan Afrika ta Kudu Thembinkosi Lorch, yayin kokarin zarta takwaransa na Masar Walid Soliman a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 2019. eNCA

Tsohon dan wasan Afirka ta Kudu mai tsaron baya, Jethro Mohlala, ya ce yan wasan Najeriya Super Eagles, za su sha wahala matuka yayin fafatwar da za su yi ranar laraba a zagayen kwata final na gasar cin kofin Afrika.

Talla

A cewar Mohlala, tsananin zafin nama da kuma iya sarrafa kwallon yan wasan Afrika ta Kudu BafanaBafana, ne zai yi matukar jigata yan Najeriya idan basu maida hankali ba.

A ranar asabar Afrika ta Kudu ta doke Masar da 1-0, abinda ya kawo karshe sanya kasar mai masaukin baki, cikin wadanda za su iya lashe kofin gasar ta bana.

Yayin sharhi kan kwazon yan kasar tasa ne kuma Mohlala ya ce, alamu sun bayyana cewa, Afrika ta Kudu na wahalar da kasashen arewacin Afrika da na yammacin nahiyar idan suka gauraya a fagen kwallon kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI