Najeriya-Buhari

Buhari zai mika sunayen sabbin ministocinsa ga Majalisa

shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari AFP/Audu MARTE

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fitar da sunayen sabbin ministocinsa da za su tafiyar da gwamnati a sabin wa’adinsa na shekaru 4 masu zuwa cikin nan da ake ciki.

Talla

Yayin zaman majalisar dattijan kasar da ke gudana a yau Laraba, shugaban Majalisar Ahmed Lawal ya ce, Buharin zai mikawa Majalisar jadawalin sunayen wadanda ya ke son ta amince ya nada su ministoci.

A cewarsa, Fadar shugaban Najeriyar na aikin tukuru ne wajen ganin sunayen da za ta gabatarwa, Majalisar sun samu wucewa kai staye ba tare da tangarda ba.

Jawaban na Ahmed Lawal dai na matsayin martini ga bukatar da Sanata Bassey Akpan ya gabatar gaban zaman majalisar.

Shugaban Majalisar Dattijan ta Najeriya ya tabbatarwa Majalisar da ma sauran daidaikun ‘yan kasar cewa Muhamamdu Buhari ya aike da sunayen ministocin kafin karewar makon nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI