Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar shari’a ta bukaci Buhari ya tabbatar da Mai shari’a Tanko Muhammad

Ibrahim Tanko Muhammad  Babban jojin Najeriya
Ibrahim Tanko Muhammad Babban jojin Najeriya NAN
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa | Bashir Ibrahim Idris
1 Minti

Hukumar dake kula da ayyukan shari’a a Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da nadin Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin Babban jojin kasa.

Talla

Daraktan yada labaran hukumar, Soji Oye yace hukumar ta amince da haka ne wajen taron da tayi a wannan makon, a karkashin jagorancin Mai shari’a Umaru Abdullahi wanda ya amince da matakin bayan tantance sunayen mutane biyu da aka gabatar musu.

Shugaban Najeriya ya nada Mai Shari’a Tanko Muhammed ne ranar 25 ga watan Janairu domin maye gurbin Walter Onnoghen da aka tuhuma da laifin kin bayyana kadarorin da ya mallaka da kuma boye wasu asusun ajiyar kudaden kasashen waje da ya mallaka sabanin dokar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.