Afrika

Oxfam ta koka da ta'azarrar matsalar rashin daidaito a yammacin Afrika

Rahoton Oxfam ya sanya kasashen Najeriya, Nijar da kuma Saliyo a jerin matakin farko da basa yunkurin samar da daidaito tsakanin al'ummarsu.
Rahoton Oxfam ya sanya kasashen Najeriya, Nijar da kuma Saliyo a jerin matakin farko da basa yunkurin samar da daidaito tsakanin al'ummarsu. Albert Gonzalez Farran / AFP

Wani rahoton kungiyar Oxfam mai rajin yaki da rashin adalci talauci da kuma habaka ci gaba, ya nuna yadda kasashen yammacin Afrika ke matukar shan wahala sanadiyyar rashin daidaito tsakanin al’umma wanda ke da nasaba da yadda gwamnatocinsu ke gaza daukar matakan magance matsalar tattalin arzikin da ta dabaibaye su, baya ga tsadar rayuwa da ke barazana ga al’ummar kasashen.

Talla

Rahoton kungiyar ta Oxfam wanda ya mayar da hankali kan yadda al’umma yammacin Afrika ke matukar wahaltuwa, musamman sanadiyyar rashin daidaito, baya ga rashin katabus din shugabanninsu wajen fitar da al’umma daga matsin rayuwa, ya ce duk da yadda tattalin arzikin kasashen ke habaka cikin sauri har yanzu kalilan ne na al’ummar su kan iya cin gajiyar ci gaban.

Cikin rahoton na Oxfam wanda kungiyar ta Fitar a jiya Talata, ya ce rashin daidaito ya kai kololuwa a kasashen na yammacin Afrika ta yadda kashi 1 na al’ummar yankin ne ke rike da galibin arzikin kasashen.

Haka zalika rahoton ya nuna kasashen yammacin Afrika a matsayin kashin baya wajen rasa ingantaccen Ilmi kulawar lafiya ko kuma kwararan ayyukan dogaro da kai don samun rayuwa mai inganci.

Rahoton na Oxfam ya gwada misali da yadda arzikin wasu attajiran mutane 5 kacal a Najeriya ya zarta ilahirin kasafin kudin kasar na 2017.

Acewar daraktan kungiyar mai kula da yammacin Afrka Adama Coulibaly Kasashe irinsu Najeriya Nijar da Saliyo su ne na gaba gaba wajen gaza samar da daidaito tsakanin al’umma yayinda rahoton ya bayyana kasashen Senegal Mauritania da Cape Varde a matsayin wadanda ke kokarin kawar da matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.