Faransa-Libya

Libya: Faransa ta amsa batun gano makamanta a sansanin sojin Haftar

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Johanna Geron

A Karon farko gwamnatin Faransa ta amsa cewa an samu makaman ta a wani sansanin sojin Janar Khalifa Haftar da ke kokarin kwace iko da birnin Tripoli na kasar Libya, dai dai lokacin da rikicin kasar ke kara tsanata.

Talla

Ma’aikatar tsaron Faransa ta shaidawa Jaridar New York Times cewar wani makami mai linzami da ake kira ‘Javelin’ irin wanda Amurka ke kerawa da aka samu a wani sansanin sojin da ke kudan Tripoli a watan Yuni, ita ta saye shi.

Sai dai gwamnatin ta ki yadda da zargin cewar ita ke bai wa dakarun Janar Khalifa Haftar makamai, matakin da ya sabawa dokar Majalisar Dinkin Duniya na takunkumin da aka sanyawa Libya, inda ta ce makaman sun bata ne a hannun dakarun ta lokacin da suke aiki a kasar.

Gwamnatin ta kara bayanin cewar, makaman sun daina aiki kuma ana shirin lalata su ne, abinda ya sa aka jibge su a wani dakin aje kayayyaki, amma ba wai an mikawa 'yan tawaye bane.

An dai gano wadannan makamai masu linzami da kudin su yakai Dala dubu 170,000 lokacin da dakarun gwamnatin Libya suka murkushe na Khalifa Haftar a sansanin su da ke Gharyan, mai tazarar kilomita 100 daga birnin Tripoli.

An dai nunawa manema labarai wadannan makamai da kuma wasu da China ta kerawa Daular Larabawa da ke dauke da sunan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.