Afrika

An murkushe yunkurin juyin mulki a Sudan

Masu zanga-zanga a kasar Sudan
Masu zanga-zanga a kasar Sudan REUTERS/Umit Bektas

Shugabanin Majalisar mulkin sojin Sudan sun sanar da cewar sun murkushe wani yunkurin juyin mulkin da bai samu nasara ba a kasar, kuma yanzu haka sun kama manyan hafsoshi 12 da kanana 4.

Talla

Wannan sanarwar na zuwa ne mako guda bayan cimma yarjejeniya tsakanin sojin da shugabannin masu zanga zanga na kafa gwamnatin rikon kwarya.

Janar Jamal Omar dake majalisar mulkin sojin yace an kama manyan sojoji daga rundunar sojin da hukumar leken asiri da kuma yan sandan farin kaya da suka yi yunkurin, cikin su harda wadanda suka yi ritaya.

Janar Omar ya bayyana cewar wannan wani yunkuri ne na dakile shirin kafa gwamnatin rikon kwaryar da aka amince da ita a kasar ta Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.