Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Bozize zai koma gida domin tsayawa takara

Tsohon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, François Bozizé, 8 ga watan janairu 2013.
Tsohon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, François Bozizé, 8 ga watan janairu 2013. AFP/Sia Kambou

Jam’iyyar tsohon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Francois Bozize, ta ce tsohon shugaban zai koma gida a cikin kwanaki masu zuwa tare da shiryawa tsayawa takara a zaben da za a yi cikin watan disambar shekara ta 2020 a cewar Sakataren jam’iyyar Christian Guenebem.

Talla

To sai dai wasu bayanai na cewa da wuya Bozize ya iya komawa a kasar, lura da cewa an kawace masa Passport, yayin da a hannun daya Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba masa takunkumi saboda rawar da ya takara a rikicin kasar.

Karkashin dokokin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dole ne dan takarar ya kasance zaune ciikin kasar tsawon shekara daya kafin zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI