Isa ga babban shafi
Ebola

Ebola ta bulla a birnin Goma

Wasu daga cikin ma'aikatan kungiyar bada agaji ta Red Cross, da ke taimakawa masu cutar Ebola a Jamhuriyar Congo.
Wasu daga cikin ma'aikatan kungiyar bada agaji ta Red Cross, da ke taimakawa masu cutar Ebola a Jamhuriyar Congo. AFP/ISAAC KASAMANI
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman | Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

Hukumomin Lafiya a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun sanar da cewa a karon farko an samu wanda ya kamu da cutar Ebola a Goma, birni na biyu mafi girma da ke kasar.

Talla

Ma’aikatar lafiyar tace wani Fasto ne ya kamu da cutar, kuma ana kyautata zaton ya dauke ta ne daga mutanen da yake mu’amala da su a coci.

Rahotanni sun ce an fara ganin alamun cutar a jikin Faston ranar Talatar da ta gabata a garin Butembo, daya daga cikin garuruwan da suka yi fama da cutar, kafin ya koma Goma a motar safa.

Hukumomin sun ce yanzu haka ana kula da fasinjoji 18 da direbar motar da ya dauke shi daag Butembo zuwa Goma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.