Wasanni

Za a tantance zakarar kwallon Afrika ta bana tsakanin Algeria da Senegal

Dan wasan Algeria Riyad Mahrez (daga dama) yayin murnar kwallon daya jefa a ragar Najeriya.
Dan wasan Algeria Riyad Mahrez (daga dama) yayin murnar kwallon daya jefa a ragar Najeriya. AFP

Algeria da Senegal sun samu nasarar kaiwa matakin wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika, bayan doke Najeriya da Tunisia a fafatwar da suka yi jiya.

Talla

Algeria tasamu nasararta ce da 2-1, ta hannun dan wasan Najeriya Troost-Ekong da ya jefa kwallo a ragarsu bisa kuskure, sai kuma dan wasan kasar ta Algeria Riyad Maharez da ya jefa kwallo ta biyu a mintunan karshe bayan samun damar bugun tazara.

A bangaren Najeriya kuwa Odion Ighalo ne ya jefa mata kwallo a ragar Algeria.

Ita kuwa Senegal ta yi nasarar doke kasar Tunisia ce da 1-0.

Da fari kasashen sun fafata wasan tsawon mintuna 90 ba tare da samun nasarar jefa kwallo a ragar juna ba, duk da cewa kowannensu ya samu damar bugun daga kai sai mai tsaron raga.

A karin lokacin mintuna 30 ne Senegal ta samu nasara, bayanda dan wasan Tunisia Dylan Bronn yayi kuskuren jefa kwallon a ragarsu.

A yanzu za a fafata wasan neman na uku ranar laraba 17 ga watan Yuli, tsakanin Najeriya da Tunisia, sai kuma tantance kasar daza ta zama zakarar bana a gasar cin kofin Afrika tsakanin Algeria da Senegal a ranar Juma’a 19 ga watan na Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.