Ahmad Tijjani Lawal kan yarjejeniyar kafa gwamnatin rikon kwarya a Sudan

Sauti 03:52
Wasu 'yan Sudan yayin murnar cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin rikon kwarya tsakanin sojoji da fararen hula.
Wasu 'yan Sudan yayin murnar cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin rikon kwarya tsakanin sojoji da fararen hula. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah

Sojoji da kuma masu fafutukar shimfida tsarin dimokuradiyya a Sudan, laraba sun rattaba hannu kan yarjejeniyar raba da madafun iko a tsakaninsu.Tun ranar 5 ga wannan wata ne bangarorin biyu suka cimma jituwa a tsakaninsu kan yadda za a raba mukaman, inda a yau suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, wadda a karkashinta fararen hula ke da wakilai 6 yayin da sojoji ke da kujeru 5.Kan haka ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Ahmad Tijjani Lawal, mai sharhi kan lamurran yau da kullum a birnin Kano.