Tafkin Chadi

Taron gwamnonin da ke kewayen Tafkin Chadi ya kankama

Wani sashi na kauyen Ngouboua, da ke yankin Tafkin Chadi.
Wani sashi na kauyen Ngouboua, da ke yankin Tafkin Chadi. REUTERS/Emmanuel Braun/File Photo

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane kusan miliyan 3 dake zama kusa da tafkin Chadi ne ke bukatar kariyar tsaro da kuma tallafi sakamakon illar rikicin Boko Haram.

Talla

Daraktan Hukumar Ci gaba na Majalisar da ke kula da Afirka, Ahunna Eziakonwa ce ta bayyana haka wajen taron Gwamnonin da ke kewaye da Tafkin Chadi da kuma masana harkar tsaro da wakilan kungiyoyin fararen hula a Nijar.

Taron da hukumar dake kula da tafkin Chadi ta shirya tare da taimakon Majalisar Dinkin Duniya zai mayar da hankali ne kan matsalar da rikicin book haram ya haifar a Yankin da kuma lalubo hanyar rage radadin matsalar ga mazauna yankin.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniyar, Ahunna Eziakonwa tace rikicin na boko haram bayan sanadiyar rasa dimbin rayuka da kuma asarar dukiyoyi, ya kuma lalata dangantakar dake tsakanin al’ummomi da kuma jefa rayuwar talakawa cikin mawuyacin hali.

Jami’ar tace mutane miliyan 19 ke rayuwa kusa da tafkin Chadi daga Jihohi 8 na kasashe 4 dake dake da al’adu da yare da kudin bai daya da suke musaya a tsakanin su.

Eziakonwa tace da taimakon kasashen Jamus da Sweden, Majalisar Dinkin Duniya na daukar matakan tallafawa mazauna wannan yankin daga kasashe 4 dake kewayen tafkin Chadin domin inganta rayuwar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.