Sudan

Masu zanga-zanga a Sudan sun dakatar da tattaunawa da gwamnati

Dubun dubatar masu zanga-zanga yau Juma'a a Sudan
Dubun dubatar masu zanga-zanga yau Juma'a a Sudan REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah

Shugabannin masu zanga zangar Sudan sun sanar da dakatar da shirin tattaunawar da za suyi yau da shugaban sojin kasar domin kammala shirin kafa gwamnatin rikon kwaryar da ake shirin kafawa.

Talla

Daya daga cikin fitattun shugabannin masu zanga zangar, Omar al-Digier ya ce an dage tattaunawar ce domin samun Karin lokaci a cigaba da tintibar juna domin daukar matsayin bai daya.

Ranar larabar da ta gabata, bangarorin biyu suka bayyana samun gagarumar nasara a ganawar da suka yi, inda suka tsayar da yau juma’a a matsayin ranar kammala tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.