Isa ga babban shafi

Sojin Najeriya da dama sun mutu a harin Boko Haram

Wasu Sojin Najeriya
Wasu Sojin Najeriya STEFAN HEUNIS / AFP
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 min

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan wasu sojojinta da suka hada da wani Kanar da Kyaftin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi. Mataimakin Darakta na Runduna Operation Lafiya Dole, Kanar Isa Ado ya bada tabbacin haka a wata sanarwa yau Juma’a a Abuja.

Talla

Kanar Ado y ace lamarin ya auku na a ranan Laraba a yankin Jakan na jihar Bornon Najeriya, lokacin da sojojin ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, inda ‘yan ta’addan suka musu kwanton bauna, sai dai ya ce dakarun Bataliya ta 212 da aka girke a Jakana sun murkushe maharan.

A cewarsa, da misalin karfe 7 saura kwata na yamma ne ‘yan ta’addan, suka zo da motoci masu bindigogi, suka yi darar mikiya kan bataliyar sojin Najeriya, amma dakarun suka yi tsayuwa irin ta daka suka murkushesu, wasu daga cikinsu kuma suka tsere, daga nan ne wadannan jami’en nata suka yi rashin sa’a, suka fada cikin kwanton baunar da masu tserewar suka yi.

Sanarwa ta ce babban hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya jajanta wa iyalan mazan da suka kwanta dama, sannan ya jaddada cewa rundunar sojin kasar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a yakin da take da ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin kasar.

Daruruwan sojoji ne suka shahada tun da kungiyar Boko Haram ta fara mayar da hankali da kai hari kan sansanonin soji a watan Yulin shekarar 2018, ciki har da manyan hafsoshi da kwamandoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.