Habasha

Tarzomar masu 'yan aware ta kai ga kisan mutum 4 a Habasha

Firaministan Habasha Abiy Ahmed
Firaministan Habasha Abiy Ahmed AFP/Monirul BHUIYAN

Akalla Mutane 4 suka mutu sakamakon harbin bindiga a kudancin a Birnin Hawassa da ke kasar Habasha inda aka samu arangama tsakanin masu goyan bayan ballewar Yankin da jami’an tsaro.

Talla

Kafofin yada labaran kasar sun ce jami’an tsaro sun kama mutane da dama yayin gudanar da zanga zangar 'yan awaren a yankin kudancin kasar.

Kabilar Sidama, wadda ita ce tafi yawan jama’a a kudancin Habasha na bukatar yancin cin gashin kai, daya daga cikin matsalolin siyasar da yanzu haka suka mamaye gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed.

Ko a watan jiya, sai da kasar ta Habasha ta fuskanci yunkurin juyin mulki da ya kai ga tashin hankali a kasar, wadda ke farfadowa daga rikicin kabilanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI