Afrika

Talauci tsakanin al'ummar Afrika ya tsananta - Rahoto

Yankin Mabella da ke Freetown babban birnin kasar Saliyo. 13/3/2008.
Yankin Mabella da ke Freetown babban birnin kasar Saliyo. 13/3/2008. REUTERS/Katrina Manson

Wata Sabuwar kididdigar masana tattalin arziki na kasa da kasa, ta nuna cewa adadin mutanen da ke fama da matsanancin talauci a nahiyar Afrika ya kai matakin ha’ula’i.

Talla

Masanan sun kara da cewa, matsalar za ta ci gaba da tsananta, saboda saurin karuwar yawan al’umma da nahiyar za ta fuskanta a shekaru 10 da ke tafe.

Yayin wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na AFP, sabon shugaban bankin duniya David Malpass ya ce kalubalen da ke fuskantar nahiyar ta Afrika ba karami bane, dan haka akwai bukatar ware kudade masu yawan gaske da kuma tsara hanyoyin samar da guraben ayyukanyi, da kuma ababen more rayuwa, domin tafiya dai dai da karuwar yawan al’umma a Afrika.

Sakamakon wani bincike da bankin Duniya yayi a shekarar 2015, ya nuna cewa matsalar talauci ta ja baya a sassan duniya da akalla kashi 10 cikin 100, sai dai a Afrika abin ba haka yake ba, domin kuwa a shekarar ta 2015, rabin wadanda ke fama da matsanancin talauci a duniya na zaune ne a nahiyar.

Hasashen masana ya kuma ce nan da shekarar 2030, kusan mutane 9 daga cikin 10 da ke kangin talauci a duniya za su fito ne daga Afrika.

Hakan ce ta sa asasun bada lamuni na duniya bayyana bukatar samar da guraben ayyunkan yi akalla miliyan 20 a nahiyar, domin rage yawan al’ummar nahiyarta Afrika da ke cikin kangin talauci, da adadinsu ya kai akalla miliyan 700.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI