Afrika ta Kudu

Zan shigar da kara kan zargin da ake yi min na rashawa-Ramaphosa

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa REUTERS/Sumaya Hisham

Shugaban Kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce, zai ruga kotu domin kalubalantar wani rahotan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da ya zarge shi da yin karya wajen karbar wasu kudaden da suka kai Dala dubu 36 daga wani kamfani a  lokacin yakin neman zabensa.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai, shugaba Ramaphosa ya ce, bayan dogon nazari kan rahotan da shugabar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Busisiwe Mkhwebane ta gabatar, ya gano cewar rahotan na cike da kura-kurai saboda haka zai je kotu domin kalubalantar sa.

Shugaban na Afrika ta Kudun ya ce, zargin da ake masa na da tsauri saboda haka ba zai bata lokaci wajen daukar mataki akai ba.

A ranar Juma’ar da ta gabata, Busisiwe Mkhwebane ta zargi shugaban da yi wa 'yan majalisu karya da gangan kan gudumawar da wani kamfani ya ba shi na Dala dubu 36 a lokacin yakin neman zabe.

Mkhwabena ta ce, da farko Ramaphosa ya ce, an bai wa dansa kudin ne, amma kuma daga bisani ya amsa cewar gudumawa ce domin takarar shugabancin Jam’iyyar ANC da yake yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI