Kamaru

Jami'an tsaron Kamaru sun dakile tarzomar gidan yarin Yaounde

Gidan Yarin Kondengui da ke Yaounde babban birnin kasar Kamaru.
Gidan Yarin Kondengui da ke Yaounde babban birnin kasar Kamaru. Journal du Cameroun

Jami’an tsaron kasar Kamaru sun yi amfani da karfi wajen kwantar da wata tarzoma da ta tashi a gidan yarin Yaounde daren jiya, bayan sun cinna wuta a gidan kason.

Talla

Masu zanga zangar wadanda akasarin su masu adawa da gwamnatin kasar ne da yan aware daga bangaren masu amfani da Turancin Ingilishi sun dauki hotan boren inda suka yada shi a kafofin sada zumunta.

Rahotanni sun ce mutane da dama sun samu raunuka cikin su harda tsohon Fira minista Inoni Ephraim da tsohon minister Urbain Olenguena Awono da masu boren suka kaiwa hari.

A shekarar 2016 aka zartas da hukuncin daurin shekaru 20 kan tsohon Fira Minista Inoni Ephraim, bayan samunsa da laifukan cin hanci da rashawa.

Babu wani fursuna da yayi nasarar tserewa daga gidan Yari, ta hanyar fakewa da tashin hankalin da ya auku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.