Amurka- Najeriya

Amurka ta haramta Visa ga 'yan Najeriya masu karya tsarin dimokaradiya

Tun a watan Janairu na 2019 Amurka ta yi gargadin haramta Visa ga 'yan Najeriyar da ke yiwa dimokaradiya zagon kasa.
Tun a watan Janairu na 2019 Amurka ta yi gargadin haramta Visa ga 'yan Najeriyar da ke yiwa dimokaradiya zagon kasa. Sputnik International

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace ta kaddamar da wani shirin hana ‘yan Najeriya da ke yiwa dimokiradiya zagon kasa lokacin zaben shugaban kasa da ‘yan majalisu izinin shiga kasar.

Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar Morgan Ortagus, ta ce wadannan mutane sun aikata laifukan kama karya lokacin zaben da ya gabata da suka hada da take hakkin Bil Adama.

Ortagus ta ce shirin ya shafi wasu ‘yan siyasa ne, banda sauran ‘yan Najeriya da kuma zababbun shugabanin da ke gwamnati.

Sai dai sanarwar bata bayyana sunayen mutanen da haramcin shiga Amurkan ya shafa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI