Uganda

Fitaccen mawakin Uganda zai yi takarar shugaban kasa

Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine
Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine © AFP

Fitaccen mawakin Uganda da ya rikide zuwa babban mai adawa da gwamnatin kasar, Bobi Wine, ya sanar da aniyar tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a yi a shekarar 2021. Mawakin ya bayyana aniyar tasa ce a yayin jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke birnin Kampala.

Talla

Bobi Wine wanda asalin sunansa shi ne Robert Kyagulanyi, ya rikide zuwa cikakken dan siyasa ne a shekarar 2017, lokacin da ya samu nasarar lashe zaben dan majalisa, abinda ya ba shi damar karfafa sukar da yake yi wa manufofin shugaban Uganda Yoweri Museveni.

Sau biyu ana kama Bobi Wine a shekarar 2018, cikin watannin Afrilu da Agusta sakamakon jagorantar zanga-zangar adawa da Museveni.

Bayyana aniyar kalubalantar shugaban na Uganda mai ci a zaben 2021 da Bobi Wine ya yi, ya kawo karshen mamaye fagen adawar kasar na tsawon shekaru akalla 20 da jagoran 'yan adawa Kizza Besigye ya yi, tsohon aboki kuma likita ga shugaba Yuweri Museveni da ya gaza lashe zaben shugabancin kasar har sau hudu.

A farkon shekarar da muke ciki kotun kolin Uganda ta tabbatar da hukuncin soke tsarin kayyade shekarun kasa da 75 ga wadanda ke shawa’ar tsayawa takara, abinda ya bai wa Museveni damar ci gaba da mulki bayan shafe shekaru akalla 30 akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI