G5 Sahel

Rundunar sojin kasashen G5 Sahel ta nada sabon Kwamanda

Daya daga cikin dakarun sojin Mali, yayin sintirin hadin gwiwa da sojojin Faransa.
Daya daga cikin dakarun sojin Mali, yayin sintirin hadin gwiwa da sojojin Faransa. REUTERS/Benoit Tessier/File Photo

Rundunar Sojin kasashen G5 Sahel da ke yaki da ‘yan ta’adda a Mali, ta nada Janar Oumarou Namata Gazama, Mataimakin Babban Hafsan sojin Nijar a matsayin sabon kwamandan rundunar domin maye gurbin Janar Hanena Ould Sidi daga Mauritania wanda yake rike da mukamin tun daga watan Yulin bara.

Talla

Shi dai Janar Gazama wanda aka karawa girma zuwa Birgediya Janar a watan Janairun shekarar 2017, an nada shi Mataimakin Babban Hafsan sojin Nijar ne a watan Janairun bara.

Rahotanni sun ce, Janar Gadzama ya taka gagarumar rawa wajen yakin da sojin Nijar keyi da mayakan kungiyar Boko Haram.

Nadin sa sabon shugaban rundunar G5 sahel, na zuwa ne gabanin babbar taron kungiyar a watan Satumbar mai zuwa a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, wanda zai maida hankali kan matsalar tsaro na kasashen yammacin Afirka 15 wato Ecowas.

Kungiyar G5 sahel mai kunshe da kasashen yankin 5, da suka hada da Maurtaniya da Mali da Nijar da Burkina Fasa da kuma Chadi, an kaddamar da ita a shekarar 2015, da taimakon kasar Faransa da ta tura dakarun Barkhan yankin domin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi, amma sai a shekarar 2017 aka karfafa ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.