Isa ga babban shafi
Tunisa

Takaitaccen tarihin tsohon shugaban Tunisia Beji Essebsi

Marigayi shugaban kasar Tunisa Beji Caid Essebsi
Marigayi shugaban kasar Tunisa Beji Caid Essebsi REUTERS/Zoubeir Souissi
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Shugaban kasar Tunisia Beji Caid Essebsi da ke matsayin shugaba mafi tsufa a duniya ya mutu yau Alhamis ya na da shekaru 92 a duniya bayan fama da rashin lafiya.

Talla

Tsohon shugaban na Tunisia Beji Caid Essebsi, cikakken sunansa shi ne Mohamed Caid Essebsi, an haifeshi ranar 29 ga watan Nuwamban 1926 a yankin Sidi Bou Said kuma shi ne shugaban kasar Tunisa na 5 haka zalika zababben shugaba na farko a tarihin kasar.

Shugaban wanda ya rike mukamin ministan harkokin wajen kasar a shekarar 1981 har zuwa 1986 shi ne Firaminista tun daga watan Fabarairun 2011 har zuwa Disamba kafin karbar ragamar shugabancin kasar a shekarar 2014.

Mohamed Caid wanda jika ne wajen Ismail Caid Essebsi da ya mulki kasar tun a karni na 19, ya fara harkokin siyasa ne tun ya na da karancin shekaru a duniya, kuma ya na da yara 4 da suka kunshi mata 2 da maza guda 2.

Mulkin Essebsi wanda ke zuwa bayan juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin tsohon shugaba Zainul Abidina bin Ali, ya gamu da matsalolin tsaro da ya haifar da hare-haren ta’addanci a sassan kasar.

Rasuwar shugaban bayan fama da rashin lafiya dai, na zuwa ne dai dai lokacin da ake shirye-shiuryen gudanar da babban zabe a cikin watan Nuwamba mai zuwa.

Mohamed Caid Essebsi shi ne ya assasa jam’iyya Nidaa Tounes da ya sauya akalar shugabancin kasar bayan samun gagarumar nasara a shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.