Morocco

Laka ta binne mota dauke da fasinjoji

Yadda zaftarewar kasa ta tafka barana a garin Pantukan da ke kasar Philippines.
Yadda zaftarewar kasa ta tafka barana a garin Pantukan da ke kasar Philippines. REUTERS/Stringer

Hukumomin kasar Morocco sun ce jami’an agaji na aikin neman wata mota dauke da fasinjoji tsakanin 16 zuwa 20, da zabtarewar kasa ta binne, sakamakon ruwan sama da aka samu a Yankin Marrakesh.

Talla

Shaidun gani da ido sun ce hadarin ya auku ne a Yankin Asni, lokacin da motar ke kan hanyar zuwa kauyen Talioiuine daga Casablanca da ke da nisan kilomita 670.

Hukumomin kasar sun ce ruwan da zabtarewar kasa ya samar da lakar da tudunta ya kai mita 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI