An yi nasarar tsamo gawar 'yan cirani 62 a tekun Mediterranean

Yanzu haka dai jami'an agaji na ci gaba da aikin ceto mutanen da suke nutse a cikin tekun
Yanzu haka dai jami'an agaji na ci gaba da aikin ceto mutanen da suke nutse a cikin tekun FETHI BELAID / AFP

Masu aikin ceto a Libya sun yi nasarar tsamo gawarwakin mutane 62 da ke cikin jirgin ruwan ‘yan ciranin da ya yi hadari a tekun Mediterranean akan hanyarsu ta zuwa nahiyar Turai.

Talla

Rahotanni daga Libya sun bayyana cewa Jirgin na dauke da ‘yan cirani fiye da 400 kuma tun a jiya jami’an tsaron gabar teku a kasar sun yi nasarar ceto mutane 145 yayin da ake da tabbacin adadin wadanda suka nutse ya iya haura 300.

A cewar Abdelmoneim Abu Sbeih shugaban sashen agajin gaggawa na kungiyar Red Crescent jami’ansu sun tsamo gawarwakin mutane 62 daga jiya zuwa yau, yayinda su ke ci gaba da aikin laluben wadanda suka nutse a kasan ruwa.

Shugaban na Red Crescent a Libya, ya ce ya zuwa yanzu baza su iya hakikance adadin mutanen da suka bace a hadarin jirgin ruwan ba, wanda ke dauke da ‘yan cirani daga kasashen Afrika da Asiya daban-daban.

A cewar kungiyar agaji ta likitoci ta kasa da kasa wato Doctor Without Borders, hadarin wanda ya faru sanadiyyar lodin da aka yiwa jiragen kwale-kwalen guda 3 da ya wuce kima, shi ne mafi muni a bana la’akari da yadda kawo yanzu aka gaza sanin hakikanin adadin mutanen da ke cikin kwale-kwalen 3.

Shima dai da yak e mika sakon jajensa game da hadarin Shugaban hukumar kula da ‘yan cirani ta majalisar dinkin duniya Flippo Grandi ya ce hadarin shi ne mafi tayar da hankali a bana.

Nutsewar kwale-kwalen 3 dauke da ‘yan cirani fiyeda 400 dai na zuwa ne bayan makamancinsa a makwanni baya da ya hallaka mutane 68 a gabar tekun Mediterranean ta bangaren Tunisia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI