Najeriya

Boko Haram ta kashe farar hula dubu 27 a shekaru 10 a Najeriya- MDD

Wasu fararen hula da Boko Haram ta yi garkuwa da su bayan samun nasarar ceto su da sojin Najeriya suka yi
Wasu fararen hula da Boko Haram ta yi garkuwa da su bayan samun nasarar ceto su da sojin Najeriya suka yi Reuters/Stringer

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa fiye da fararen hula dubu 27,000 rikicin boko haram ya hallaka a Yankin arewa Maso Gabashin Najeriya a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Talla

Jami’in Majalisar da ke kula da aikin jinkai a Najeriya, Edward Kallon ya bayyana haka, wajen wani taron tunawa da wadanda suka mutu a rikicin da aka yi a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja babban birnin kasar.

Kallon ya bayyana harin Nganzai da aka samu a makon jiya a matsayin daya daga cikin hare hare mafi muni a baya bayan nan.

Jami’in Majalisar Dinkin Duniyar ya ce a cikin watannin da suka gabata, akalla mutane sama da 130,000 suka tsere daga matsugunan su sakamakon hare haren kungiyar, yayin da ya jajantawa ma’aikatan agajin da suka rasa rayukan su wajen aikin taimakawa jama’ar yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.