Cutar Kyanda ta hallaka yara 100 a arewa maso gabashin Najeriya

Rahoton ya bayyana cewa mace-macen sun faru ne tsakanin watan Janairu zuwa Yunin shekarar nan
Rahoton ya bayyana cewa mace-macen sun faru ne tsakanin watan Janairu zuwa Yunin shekarar nan AFP Photo/ASHRAF SHAZLY

Wani bincike a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya nuna yadda cutar kyanda ta hallaka mutane 100 cikin mutane fiye da dubu 21 da suka kamu da cutar cikin watannin baya-bayan nan.

Talla

Wani bincike da kamfanin dillancin labaran Najeriyar NAN ya gudanar a jihohin Bauchi Borno Yobe da kuma jihar Gombe ya nuna cewa akwai adadin mutane dubu 21 da 11 da yanzu haka ke fama da cutar ta kyanda, ko da dai ya ce babu masu fama da ita a jihohin Adamawa da Jigawa duk kuwa da makwabtakarsu da jihohin da ke fama da cutar.

A jihar Borno binciken ya bayyana cewa a can lamarin ya fi kazanta da adadin mutane dubu 18 da 204 da ke fama da cutar baya ga mutane 93 da cutar ta hallaka galibi kananan yara.

Binciken na NAN ya ruwaito shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Borno Sule Mele na cewa cutar ta fi tsananta a sansanonin ‘yan gudun hijira, wanda kuma ke da nasaba da karancin daukin magungunan da suke fuskanta baya ga rashin tsaftar muhallansu.

Binciken na NAN ya kuma bayyana cewa karancin tsaro da hare-haren boko Haram na watannin baya-bayan nan ya haddasa tsaiko ga damar samun isar da magungunan jihohin musamman Borno.

Cikin kalaman Dr Mele, wanda kwararren likita ne, ya ce tsanantar cutar ya faru ne sakamakon gaza gudanar da alluran rigakafin cutar musamman a yankunan da karancin tsaro ya tsananta da kuma hare-hare.

A jihar Yobe rahoton ya bayyana adadin mutane dubu 2 da 675 da suka kamu da cutar ta kyanda baya ga wasu 7 da suka mutu tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI