Kakakin kungiyar Shi'a a Najeriya Ibrahim Musa kan matakinsu na dakatar da Muzahara

Sauti 03:33
Shugaban Mabiya shi'a na Najeriya Ibrahim El-Zakzaky
Shugaban Mabiya shi'a na Najeriya Ibrahim El-Zakzaky Guardian Nigeria

Kungiyar Shi’a a Najeriya ta sanar da dakatar da muzahar da ta ke yi domin ganin an saki shugaban ta Sheikh Ibrahim El Zakzaky. Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne domin daukar matakan shari’a kan bayyana ta a matsayin kungiyar ta’addanci da kuma tattaunawar da akeyi a bangare daya tsakanin shugabannin ta da wakilan gwamnati.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kakakin kungiyar Ibrahim Musa, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.