Lafiya

Ebola ta kashe mutane kusan dubu 2 a Congo

Jana'izar daya daga cikin wadanda Ebola ta kashe a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo
Jana'izar daya daga cikin wadanda Ebola ta kashe a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo REUTERS/Baz Ratner

Yau ake cika shekara guda da sake barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, yayinda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar cewa, mutane sama da 2,600 suka kamu da cutar, inda aka tabbatar da mutuwar sama da 1,800 a yankin Ituri da Arewacin Kivu.

Talla

Sanarwar hadin gwuiwa da shugaban Hukumar Lafiya, Tedros Adhanom Gebreyesus da shugaban Hukumar Jinkai ta Majalisar, Mark Lowcock da shugabar UNICEF Henriatta Fore da takwaransu  na Hukumar Abinci David Pearsley suka bayar game da cutar ta ce, sun gamsu da rawar da su da abokan aikinsu ke takawa wajen dakile yaduwar cutar duk da matsalolin da ake samu.

Hukumomin sun ce, bayan mutuwar mutane 1,800, hukumomin sun yi nasarar yi wa mutane sama da 170,000 rigakafi tare da mutane 1,300 da aka warkar bayan sun kamu da cutar a cibiyoyi 14 da aka kafa, yayinda aka gwada mutane miliyan 77 mazauna kasar da kuma baki.

Sanarwar ta ce, hukumomin sun samar da wuraren wanke hannaye sama da 10,000 a wurare daban daban, kana an dauki mutane sama da 2,000 aiki domin fadakar da jama’a.

Hukumomin sun ce, sun samar da abinci ga marasa lafiya 44,000 domin hana su zirga-zirga, sannan suna bai wa yaran makaranta 25,000 abinci a yankin da ake fama da matsalar cutar.

Hukumomin sun sake jaddada aniyarsu ta ci gaba da taimakawa mutanen Congo, yayinda suke jajanta musu wajen rasa rayukan da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI