Isa ga babban shafi

An kara samun wadanda suka kamu da Ebola a birnin Goma na Congo

Jami'an lafiya da ke gudanar da gwajin cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Jami'an lafiya da ke gudanar da gwajin cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo REUTERS/Djaffer Sabiti
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 3

Akalla wasu mutane 7 daga cikin iyalan mutum na biyu da Ebola ta kashe a birnin Goma na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, yanzu haka na karkashin binciken lafiya don tabbatar da ko suna dauke da cutar.

Talla

Mutanen 7 dai kari ne kan Uwargidan mutumin da ‘yarsa wadanda yanzu haka aka tabbatar da suna dauke da cutar ta Ebola, kuma su ke karbar kulawa a cibiyar kula da Ebolan da ke birnin na Goma.

Tun a ranar Larabar da ta gabata, da iyalan mutumin wanda aka bayyana da mahakin zinare suka iso birnin na Goma, hukumomin lafiya suka killacesu don gudanar musu da gwaje-gwaje.

Sai dai Dr Boubacar Diallo babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da shirin yaki da cutar ta Ebola a Kasar ta Congo, ya bayyana cewa kawo yanzu ba a ga wasu alamu da ke nuna mutanen 7 na dauke da cutar ba.

Dr Diallo na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, baya ga mutanen 7 akwai kuma Karin wasu mutum 283 da aka tabbatar da sun yi mu’amala da mutumin da matarsa da kuma ‘yarsa wadanda suma yanzu haka ke karbar kula tare da binciken lafiya da ke nufin gane ko suna dauke da cutar.

Mutuwar mutumin a ranar Larabar da ta gabata, kari ne kan mutuwar wani limamin majami’a dake matsayin majinyaci na farko da cutar ta hallaka a birnin Goma, ko da dai mahukunta sun ce babu alaka tsakanin mutanen biyu la’akari da cewa ba daga yanki daya suka fito ba.

Bullar cutar ta Ebola a birnin na Goma mai dauke da mutane fiyr da miliyan biyu ya sanya razani a zukatan jama’a har ma da makotan kasaar bisa tsoron ka da annobar cutar ta tsallaka makota.

A cewar ma’aikatar lafiyar kasar, tun bayan sake bullar cutar karo na 10 a Jamhuriyar Demokradiyyar Congon ranar 1 ga watan Agustan bara, yanzu haka ta hallaka mutane dubu 1 da 823.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana annobar cutar a wannan karon cikin kasar ta Congo a matsayin mafi muni bayan makamanciyarta da ta hallaka mutane dubu 11 a kasashen Guinea, Siraliyon da kuma Liberia cikin shekarun 2014 zuwa 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.