Nijar-Faransa

Jamhuriyar Nijar na bikin cika shekaru 59 da samun 'yancin kai

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou yayin jawabinsa a bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar daga hannun Faransa
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou yayin jawabinsa a bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar daga hannun Faransa ludovic MARIN / AFP

Yau Asabar 3 ga watan Agusta kasar Nijar ke bikin cika shekaru 59 da samun 'yancin kai daga hannun Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, bikin da a wannan karon ke zuwa dai dai lokacin da matsalolin tsaro suka dabaibaye kasar, musamman hare-haren kungiyoyin ta'addanci.

Talla

Kamar yadda aka saba bisa al'ada shugaban kasar ta Nijar kan gabatar da jawabi ga al'umma game da halin da kasa ke ciki a jajiberan wannan rana, kuma a wannan karon ma haka abin ya faru inda shugaba Mahamadou Issoufu a daren jiya Juma'a ya gabatar da jawabi kan batutuwa daban-daban.

Yayin jawabin shugaba Mahamadou Issoufou gabanin fara taron bikin ranar gadan-gadan a yau Asabar, ya yaba da nasarar da aka samu ta fuskar yaki da ta'addanci a kasar, wanda ya ce na da nasaba da tallafin dakarun ketare da kasar ke samu.

Kai tsaye shugaban na Nijar, baya ga jinjinawa dakarun Sojin kasar ya kuma yaba da kokarun dakarun rundunar Barkhane baya ga Sojin Amurka wadanda ya ce suna taimakawa matuka wajen kakkabe ayyukan ta'addanci a Nijar.

A dai irin wannan rana ta 3 ga watan kowanne Agusta da Nijar kan tuna da ranar 'yanci, hukumomi da manyan jami'an gwamnati kan yi amfani da damar wajen dashen itace da nufin magance matsalar kwararowar hamada.

Jamhuriyar ta Nijar wadda Faransa ta yiwa mulkin mallaka, a shekarar 1960 ne ta samu 'yancin kai, ko da kawo yanzu ta na jerin matalautan kasashe a Nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.