Najeriya

'Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah a Adamawa

Wasu 'yan Bindiga a Najeriya
Wasu 'yan Bindiga a Najeriya Daily Post

Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da wani farmakin ‘yan bindiga da ya kai ga kisan shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Sa’idu Kolaku.

Talla

A cewar rundunar ‘yan bindigar sun yiwa gidan Kolaku da ke yankin Sabon Pegi a karamar hukumar Mayo Belwa kawanya a yammacin jiya Asabar suka kuma harbe shi da bindiga.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan Jihar ta Adamawa Suleiman Nguroje, shugaban na Miyetti Allah Sa'idu Kolaku ya mutu bayan kai shi asibiti cikin gaggawa.

Rundunar 'yan sandan ta Adamawa wadda ta ce babu hakikanin wadanda suka kaddamar da farmakin tare da hallaka Kolaku sai dai za su gudanar da bincike don hukunta wadanda ke da hannu a kisan.

Kisan shugaban kungiyar Fulanin na zuwa a dai dai lokacin da alaka ke kara tsami tsakanin Fulanin da wasu kabilu musamman a kudancin kasar ta Najeriya da kuma wani yanki na Arewaci, tun bayan matakin gwamnati na gina musu wuraren kiwo na zamani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.