Uganda - Ebola

Uganda za ta soma gwajin allurar rigakafin cutar Ebola

Yadda jami'an lafiya ke aikin baiwa mutane rigakafin cutar Ebola a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.
Yadda jami'an lafiya ke aikin baiwa mutane rigakafin cutar Ebola a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo. REUTERS/Djaffer Sabiti

Kasar Uganda ta bayyana soma amfani da gwajin allurar rigakafin cutar Ebola, da za a yi amfani da shi a Jamhuriyar Dimikaradiyar Congo mai makwabtaka da ita, inda annobar ta Ebola ta hallaka mutane dubu 1 da 800 cikin shekara daya.

Talla

Aikin gwajin maganin rigakafin hana kamuwa da annobar ta Ebola ‘MVA-BN’ da kamfanin hada magunguna na Amruka Johnson&Johnson ya samar, zai dauki tsawon shekaru 2 ana yi, kamar yadda sanarwar da hukumar binciken magunguna ta kasar Uganda (MRC) ta sanar.

Hukumar ta MRC ta bayyana cewa tafiyar da aikin bada maganin riga kafin, zai kunshi kimanin jami’an kiyon lafiya dubu 8000, wadanda kuma ke sahun gaba a cikin aikin sun hada ne da malaman tsabta, da na motocin daukar marasa lafiya, da kuma masu kula da dakunan ajiye gawarwaki, sai kuma masu binne mamata a lardin Mbarara dake yammacin kasar ta Uganda.

Kawo yanzu dai babu maganin da zai hana kamuwa ko kuma warkar da cutar Ebola a duniya, sai dai ana da kyakkyawan fata samun maganin, la’akari da cewa akwai wasu jerin magungunan hana kamuwa da cutar ta Ebola na gwaji da ake kan samarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI