Burundi

Zazzabin cizon sauro ya hallaka kusan mutum dubu 2 a Burundi

Wasu matakan kariya daga Malaria a Burundi
Wasu matakan kariya daga Malaria a Burundi www.msf.org

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa adadin mutane dubu 1 da 800 zazzabin cizon sauro na Malaria ya hallaka cikin shekarar nan a kasar Burundi, dai dai lokacin da cutar Ebola ke ci gaba da tsananta a makociyar kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

Talla

Rahoton wanda hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta fitar a yau Talata, ta bayyana cewa akalla mutane miliyan 5 da dubu dari 7 ne suka kamu da cutar ta zazzabin Malaria wanda sauro ke haddasawa cikin shekarar nan a kasar ta Burundi.

Rahoton na OCHA ya bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar nan zuwa 21 ga watan Yulin da ya gabata, kididdiga ta nuna yadda mutane dubu 1 da dari 8 da daya suka mutu sanadiyyar Malaria.

A cewar rahoton abin takaici ne yadda cutar ta kama rabin al’ummar kasar mai yawan mutane miliyan 11 amma aka gaza sanya mata dokar ta baci tare da neman kulawar kasa da kasa don magance ta, inda hukumar ta OCHA ke cewa ta kai matakin da ya kamata ace an ayyana ta a matsayin annoba musamman a cikin watan Mayu.

Sai dai hukumar OCHA ta bayyana karancin kudaden tallafawa ayyukan lafiya a kasar, a matsayin batun da ya ta’azzara cutar baya ga, kin kulawa daga bangaren gwamnati.

Masu ruwa da tsaki a kasar dai na dora alhakin ta’azzarar cutar kan gwamnati wadda ta ki amincewa da ayyana cutar ta zazzabin Malaria a matsayin annoba saboda tsoron ka da gazawarta ya bayyana ga jama’a dai dai lokacin da ake gab da babban zaben kasar a shekara mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI