Najeriya da WHO sun kaddamar da yaki da cutuka marasa yaduwa
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Najeriya da hadin guiwan hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO ta kaddamar da wani sabon shirin yakar cututtuka marasa yaduwa da ke matukar kashe al’umma a Nigeriya.A binciken da majalisar dinkin duniya ta gudanar,ta gano cewa kashi 71 na mace-mace a duniya suna da alaka da wadannan cututtuka marasa yaduwa kamarsu hawan jini, cuwon zuciya,cutar laujen jini wato sickle cell a turance da dai sauran su. Wannan shiri da aka kaddamar za’a yishi ne na tsawon shekaru 7 wato daga 2019 zuwa 2025. Ga wakilin mu na Abuja Mohammad Sani Abubakar dauke da rahoto.
Najeriya da WHO sun kaddamar da yaki da cutuka marasa yaduwa
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu