Mutane 37 sun mutu a rikicin makiyaya a Chadi
Wallafawa ranar:
Shuagaban Chadi Idris Deby itno ya sanar da mutuwar mutane akalla 37 sakamakon wani saban rikici daya barke tsakanin manoma da makiyaya a farkon wannan makon a yankin gabashin kasar.
A cewar wata kungiya mai zaman kanta, rikicin ya samo asali ne a yankin Hamra bayan an gano gawar wani makiyayi, lamarin da ya haifar da dauki-ba-dadi tsakanin jama'arsa da manoma ‘yan kabilar Ouaddaiens.
Rikicin ya kuma ketara zuwa yankin Chokoya, inda wani basaraken gargajiya ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, an kidaya gawarwakin mutune 25.
Yankin gabashin kasar ta Tchadi, wuri ne na kiwo da ke kan iyakar kasar Sudan kuma a 'yan shekarun baya-bayan ya kasance wani yanki da ake yawaita rikici tsakani makiyaya Larabawa da mazauna yankin 'yan kabilar Ouaddaiens kan batun filayen noma da wuraren kiwo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu