Isa ga babban shafi
Faransa-Libya

An ceto karin 'yan cirani 81 a tekun Libya

Kwale - kwalen kungiyoyin aikin ceto daya ceto bakin - haure
Kwale - kwalen kungiyoyin aikin ceto daya ceto bakin - haure Anne CHAON / AFP
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 Minti

Kungiyoyin agajin Faransa, SOS Mediterranean da MSF sun ceto karin ‘yan cirani 81 a tekun Libya a yau Lahadi, wadanda suka hade da 130 da ke cikin jirgin ruwan Ocean Vikings.

Talla

Mutanen wadanda matasa ne, akasari ‘yan Sudan, da suka baro Libya a daren Asabar a wani kwale kwalen balam – balam, sun yi ta tafi da sowa yayin da suka hango jirgin tafe.

Aikin ceton na wannan Lahadi shine na uku a cikin kwanaki ‘yan kwanaki

Jirgin wanda mallakan hadin gwiwa ne tsakanin SOS Mediterranean da Medecins Sans Frontieres, ko Doctors without Borders, ya yi sintirin tekun ne har na mil 50 zuwa tekun Tripoli.

Shuagaban aikin ceto na kungiyar SOS Mediterranean, Nicholas Romaniuk ya shaida wa kamfanin dillancin labarana Faransa cewa, su kadai ne ke yankin saboda jami’en tsaron Libya ba sa kai dauki ko da an bukaci haka daga garesu.

Ya kara da cewa kyaun yanayi zai karfafa wa ‘yan ciranin shiga tekun daga Libya, bugu da kari, hutun da aka fara na babbar Sallah a Lahadin nan, wadda sanadinsa babu jami’en tsaro masu sintiri zai kara wa bakin hauren karsashin barin gari ta teku.

A ranar Juma’a, kungiyar ta ceto wasu daga yammacin Afirka akasari daga Senegal da Ivory Coast wadanda suka shiga Libya da zummar neman aiki, amma rikici ya rutsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.