Nijar

Kungiyar agaji ta MSF ta janye daga wasu yankunan jihar Diffa

Sansanin 'yan gudun hijirar da Boko Haram ta kora a jihar Diffa,kudu maso gabashin Nijar.
Sansanin 'yan gudun hijirar da Boko Haram ta kora a jihar Diffa,kudu maso gabashin Nijar. irinnews.org

A Jamhuriyar kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres ta sanar da dakatar da ayyukanta a yankin Maine-Soroa da ke jihar Diffa da ke da iyakar da Najeriya mai fama da ayyukan Boko Haram.

Talla

Daukar matakin ya biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai wa jami’an kungiyar ta MSF ne a ranar 26 ga watan afrilun da ya gabata, inda tun a wannan lokaci kungiyar ta fara nazari dangane da makoma da kuma tsaron ma’aikatanta.

MSF ta share tsawon shekaru uku tana gudanar da ayyukan jinkai musamman bangaren kiwon lafiya, kuma shugaban kungiyar reshen kasar Nijar Abdoul Aziz Mohammed ya ce dole ne su dauki wannan mataki, saboda wannan matsala ta rashin tsaro a yankin.

A yankin iyakar kasar ta Nijar da Mali ma kungiyar ta fuskanci hari daga ‘yan bindiga, lamarin ya sa ta dauki matakin yanye jami’anta daga wasu sansanonin ‘yan gudun hijirar Mali da ke cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI