Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane 8 a Najeria

Sojojin Najeriya a yankin Borno
Sojojin Najeriya a yankin Borno RFI/OR

Bayanai daga Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 8 cdiki har da sojoji uku, a harin da ‘yan Boko Haram suka kai kan sansanin soji da kuma wani kauye da ke jihar Borno.

Talla

Shaidu sun ce an kai hare-haren ne a ranar asabar da ta gabata a barikin soji da ke Gubio mai tazanar kilomita 80 daga Maiduguri inda suka kashe sojoji uku.

Fararen hula biyar ne suka rasa rayukansu a musayar wutar da aka yi tsakanin sojoji dan mayakan na reshen kungiyar Boko Haram da ake kira ISWAP.

Wadanda suka shaidi lamarin sun ce maharan sun zo ne a cikin motoci 8 da kuma manyan makamai, inda suka share tsawon awanni hudu ana musayar wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI