Cote d'Ivoire

DJ Arafat, mawakin Cote d'Ivoire ya rasu

DJ Arafat a Abidjan
DJ Arafat a Abidjan ISSOUF SANOGO / AFP

Shahrarren mawakin zamani dan kasar Cote d’Ivoire DJ Arafat ya rasu sakamakon hatsari a kan babur cikin daren Litinin a birnin Abidjan.

Talla

Arafat wanda ya yi suna sakamakon salon rawa da waka irin na coupé-décalé, yana da dimbim magoya baya a kashen duniya masamman Yammaci da Tsakiyar Afirka renon Faransa.

A ranar Litinin, kimanin masoyansa dubu 1 ne suka taro a harabar asibitin da ya ke kwance a garin Cocody na Abidjan, babban birnin Ivory Coast wurin da mawakin ya rasu.

An ji masoyan nasa suna ta kuka suna fadin cewa, “ba zai yiwu Arafat ya mutu ba”.

Rahotannin sunce mawakin kan babur yayi, yayi taho – mu - gama gaba da wata mota, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

An haifi DJ Arafat, wanda ainihin sunansa Ange Didier Huon a shekarar 1986, kuma yana da dimbim masoya a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka masu amfani da harshen Faransanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI