Afrika

Kotu za ta saurari korafi kan rashin lafiyar shugaban Gabon

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Odinba a birnin Libreville.
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Odinba a birnin Libreville. GABRIEL BOUYS / AFP

A ranar 26 ga wannan wata na Agusta ne kotun daukaka kara da ke birnin Libreville za ta saurari korafin da aka gabatar dangane da yanayin lafiyar shugaban kasar Ali Bongo ko zai iya ci gaba da mulkin kasar ko kuma akasin haka.

Talla

Bayan dawowar shugaban daga inda ya yi jinya wato kasar Maroko, jam’iyyun adawa 10 da wasu kungiyoyin fararen hula sun shigar da kara a gaban kotu inda suka bukaci a bayyana shugaban da cewa ba zai iya ci gaba da mulki ba saboda rashin lafiya, karar da za a saurar a ranar 26 ga wannan wata na agusta.

Tun da ya dawo daga jinyar da ya je kasar Morocco a watan Maris, har yanzu shugaba Bongo bai yi jawabi kai – staye ga ‘yan kasarsa ba, ko kuma ya fito bainar jama’a.

Bongomai shekaru 60, ya gaji mahaifinsa Omar Bongo,wanda ya hau karagar mulki a shekarar 1967 zuwa lokacin da ya rasu a shekarar 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI