kamaru

'Yan fashi sun yi garkuwa da Turawa a tekun Guinea

Tekun Guinea na fama da hare-haren 'yan fashin teku
Tekun Guinea na fama da hare-haren 'yan fashin teku REUTERS/U.S. Navy photo/Handout

Wata majiyar sojin ruwan Kamaru ta bayyana cewa, ‘yan fashin teku sun yi awon gaba da wasu Turawa da’Yan Asiya a tekun Guinea, kusa da yammacin tashar jiragen ruwan birnin Doula.

Talla

Wani babban jami’in sojin ruwan Kamaru ya bayyana cewa, an sace ma’aikatan jiragen ruwan ne a safiyar jiya Alhamis, amma bai yi karin bayani ba game da kasasshe ko kuma adadi na wadannan mutane da aka sace.

Rahotanni na cewa, akwai yiwuwar ‘yan fashin tekun sun fito ne daga Najeriya, kuma tuni jami’an tsaron Kamaru suka fara farautar su.

Wani jami’i da ke aiki a tashar jiragen ruwa na birnin Doula ya tabbatar da garkuwa da ‘yan kasashen ketaren, yana mai cewa, an sace su ne bayan harin da aka ka iwa jirgin da ke dauke da su.

Tekun Guinea wanda gabarsa ta ratso tun daga kasar Libya zuwa Gabon, na fama da matsalar ‘yan fashi da sace-sacen man fetur da safarar mutane da kwayoyi baya ga haramtacciyar harkar kamun kifi.

Kididdigar Hukumar Kula da Teku ta kasa da kasa ta nuna cewa, an yi garkuwa da mutane 62 a yankin tekun Guinea a ciki watanni shida na farkon wannan shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.